Hausa News

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da riga-kafin cutar Shan inna na shekarar 2025

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da gangami yaki da cutar Shan inna na shekarar 2025 a fadar Hakimin Warawa da ke karamar hukumar Warawa.

A jawabinsa, gwamana Alhaji Abba Kabir yusif Wanda ya samu wakilcin mataimakan sa kwamared Aminu Abdussalamu gwarzo ya sake jaddada kudurin gwamnatin jiha na kawar da cutar shan inna da kuma kare lafiyar yara a duk fadin jihar Kano.

Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar sun kai yaransu don karbar rigakafin allurar cutar Shan innar a lokaci aiki.

“Mun kuduri aniyar kare kowanne yaro daga cututtukan da za a iya rigakafinsu da allurar rigakafi.”

“Muna kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar da cewa dukkan yaran da ba su wuce shekaru biyar ba sun samu rigakafin polio.”

Bayan jawabin Mataimakin Gwamna, Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yaba da sadaukarwar ma’aikatan lafiya, shugabannin al,umma, da abokan hulda na ci gaba da tallafa wa kokarin yin allurar rigakafi a fadin jihar.

Sai dai, ya bayyana damuwa kan karuwar kwararar bakin haure zuwa jihar Kano ta iyakokin kauyuka, yana mai gargadin cewa cudanyar bakin haure da al’ummar gari na iya kawo cikas ga ci gaban da aka samu wajen kawar da cutar shan inna.

“Ci gaba da kwararar bakin haure tare da cudanya da al’ummomin yankunan kan iyaka na zama babbar barazana ga lafiyar jama’a.”

“Idan ba a kula ba, hakan na iya dagula nasarorin da muka samu a yaki da cutar shan inna.”

“Ina kira ga dukkan hukumomin tsaro da na lafiya da su kara kaimi wajen sa ido a kan iyakoki da kuma tabbatar da cewa dukkan yaran da suka shigo an yi musu rigakafi,” in ji Dr. Yusuf.

A lokacin kaddamar da Shirin an samu halartar manyan jami’an gwamnati, ma’aikatan lafiya, s, shuwagabannin al’umma, da jama’ar gari a wajen taron kaddamarwar.

Aikin National Immunization Plus Days (NIPDs) ya kasance wata muhimmiya dabara wajen ci gaba da kare jihar Kano daga cutar Shan inna da kuma karfafa yadda za a makance barkewar cututtuka a fadin jihar.

Gwamnatin Jihar Kano tare da hadin gwiwar abokan hulda sun dage wajen cimma burin samun lafiyayyar Al,ummar jihar Kano mai ‘yanci daga cutar shan inna.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top