Hausa News

Fusatattun matasa a Garin Rano sun ƙone Ofishin ‘yansanda -Sun jikkita DPO

Baffa Ibrahim Kano

A safiyar wannan rana ta litinin an samu hatsaniya a garin Rano , Sakamakon rasuwar wani matashi sakamakon bincike da ake   masa a Ofishin ‘yansanda wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar matashin.

Majiyarmu ta tabbatar mana cewa bayan rasuwar matashin ya  DPO ya dauki gawar matashin ya kaita gidansu. Wannan ya tunzurar al’ummar garin na Rano wanda kuma suka farwa ofishin ‘yansandan.

Haka kuma bayan da fusatattun matasan suka isa  ofishin Suka banka masa wuta suka kori jami’an ‘yansandan.

Lamarin da ya sa DPO ya fara Harbi Kuma ya yi ƙoƙarin guduwa amma duk da haka sai da Matasan suka cimmasa .kamar yadda majiyarmu ta shaida mana .

Zuwa yanzu  Kakakin Rundunar ‘yansandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin .za kuma su tabbatar da zanan lafiya ya dawo a garin Rano.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top