Hausa News

An fara biyan masu yi wa ƙasa hidima Sabon Alawus Na N77,000

Hukumar masu yi  wa ƙasa  hidima (NYSC)  ta fara biyan basussukan  alawus-  alawus na N77,000 da aka amince da su a duk wata ga masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya.

Bayanin hakan ya fito  ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar  NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, wanda ya bayyana cewa za a biya ƙudin ne   daki-daki.

 Biyan bashin kudin Alawus din wani mataki ne na   cika alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na daidaita alawus-alawus din Masu yi wa ƙasa hidima da sabon mafi ƙarancin  albashi na ƙasa —alkwarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara yi a watan Satumban 2024.

 Biyan bashin ya biyo bayan fara aiwatar da sabon alawus din ne a watan Maris din shekarar 2025. Kafin a yi ƙarin alawus din masu yi wa ƙasa hidima na   karɓar  Naira 33,000 a baya00zywa yanzu kowanne mai yi wa ƙasa hidima koda Ya kammala zai karɓi bashin adadin watannin da Yake bi .za kuma a cigaba da biyan waɗanda suke hidimar Yanzu N77,000.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top