
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birni, Kuma mai neman takarar Majalisar Tarayya a ƙaramar Hukumar ta Birni, Faizu Alfindiki Ya shirya liyafar cin abinci ga Abokansa na Siyasa da na Mu’amula da waɗanda suka taso tare .
Liyafar wadda aka gudanar a gidansa ta samu halartar mutane daga bangarorin da muka zayyano. Yayin liyafar an gudanar da addu’oin zaman lafiya a ƙasa da samun nasarar Jam’iyyar APC a shekarar 2027 a Kano da ma ƙasa .
Da yake jawabi yayin taron Faizu Alfindiki wanda kuma a halin yanzu babban mataimaki na musamman ne ga Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Hon.Tajuddeen Abbas, ya bayyana jin dadinsa Yadda abokan na sa suka amsa gayyatar da ya yi musu. Ya ce hakan ya faranta masa rai matuƙa, kasancewa akwai wadanda suke ba jam’iyyq ɗaya ba amma sun Amma gayyatar.
Alfindiki ya ƙara da cewa wannan taro an yi shi domin sada zumunci kuma zai cigaba da gudana lokaci bayan lokaci. Ya kuma godewa Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da na Jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas bisa yadda suke yin duk mai yiwuwa wajen ganin Jam’iyyar APC ta samu Nasara a shekarar 2027.
Ya ce idan har Allah Ya ba shi dama zama Ɗanmajalisa Mai wakilatar Ƙaramar Hukumar Birni a shekarar 2027 zai fito da tsare- tsaren da za su ciyar da Matasa da Mata da Dattijan Ķaramar Hukumar gaba.