Hausa News

Babban Mataimaki na Musamman ga Sanat Barau Jibrin Ya Fice daga APC

 

 

Daga Fatima Haruna Maƙoda

 

Tsohon mai bawa tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin siyasa, Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP Kwankwasiyya.

 

A wata ganawa da ya yi da magoya bayansa yau, Bakwana ya bayyana cewa ya bar jam’iyyar APC ne saboda an mayar da su saniyar ware, kuma ba su da wani matsayi mai amfani a cikin jam’iyyar.

 

Ya kara da cewa Ganduje da wasu na kusa da shi sun fi maida hankali wajen cutar da mutane da sharri maimakon su rungumi ci gaban jam’iyyar da kare muradun al’umma.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top