
Bayanan da ke fitowa daga Makusanta Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata na nuni da cewa har yanzu ba a gama cimmq matsaya kkan onda za binne shi ba.
Bayanan sun saɓa da bayanan da ake yaɗawa cewa hukumomin Saudiyya sun amince a yi janaizar Marigayin a Madina .”Har Yanzu Ba Mu Cimma Matsaya Da Gwamnatin Saudiyya Kan Batun Binne Marigayi Aminu Dantata A Can Ba, Idan Abin Ya Ja Lokaci Za Mu Dawo Da Gawarsa Kano A Yi Jana’izarsa,”Inji Sakataren Marigayin, Wato Mustapha Abdullahi Junaidu