
Hukumar masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ta fara biyan basussukan alawus- alawus na N77,000 da aka amince da su a duk wata ga masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Darakta Janar na Hukumar NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, wanda ya bayyana cewa za a biya ƙudin ne daki-daki.
Biyan bashin kudin Alawus din wani mataki ne na cika alkawarin da Gwamnatin Tarayya ta yi na daidaita alawus-alawus din Masu yi wa ƙasa hidima da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa —alkwarin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara yi a watan Satumban 2024.
Biyan bashin ya biyo bayan fara aiwatar da sabon alawus din ne a watan Maris din shekarar 2025. Kafin a yi ƙarin alawus din masu yi wa ƙasa hidima na karɓar Naira 33,000 a baya00zywa yanzu kowanne mai yi wa ƙasa hidima koda Ya kammala zai karɓi bashin adadin watannin da Yake bi .za kuma a cigaba da biyan waɗanda suke hidimar Yanzu N77,000.