Hausa News

Gawuna ya aike da saƙon ta’aziyyar ‘yan wasan Kano da suka rasu sakamakon Hatsari.

 

Shugaban Hukumar Gudanarwa ta Bankin Lamuni na Gidaje na Tarayya (FMBN) kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Bayero, Kano, Mai Girma Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana alhinin sa dangane da rasuwar ‘yan wasan Kano guda ashirin da daya (21) da suka rasa rayukansu a wani hadarin mota yayin dawowa daga gasar wasannin kasa da aka kammala a garin Abeokuta, Jihar Ogun.

 

A wata sanarwa da ya fitar ga kafafen yada labarai na cikin jihar da ƙasa baki ɗaya, Dr. Gawuna ya bayyana lamarin a matsayin “babban iftila’i” kuma babban rashi ne ga al’ummar Jihar Kano.

 

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan wasan ke dab da komawa gidajensu domin haɗuwa da iyalansu, abokansu da masoyansu bayan wakiltar jihar a gasar wasannin da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu.

 

“Abin tausayi sosai a rabuwa da masoya a irin wannan hali,” in ji sanarwar. “Koda yake mutuwa ƙaddara ce da babu wanda zai guje mata, amma yadda wadannan matasa suka bar filin wasa cikin nishadi da ƙoshin lafiya amma daga baya suka rasa rayukansu, ya ƙara tsananta wannan alhini.”

 

Dr. Gawuna ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Kano yana mai bukatar kowa da kowa da ya dogara ga addu’a da juriya a wannan lokaci na jimami.

 

Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya jiƙan mamatan, Ya yi musu Rahama, Ya ba iyalansu hakuri da juriya, tare da yi wa wadanda ke kwance a asibiti sakamakon raunukan da suka samu addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa.

 

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top