A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2025 ne shugaba Bola Tinubu ya yi bikin cika shekaru biyu akan karagar mulki, inda ya aika da saƙo ga ‘yan Nijeriya, inda ya bayyana irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu da kuma kalubalen da ke fuskanta.
A cikin sakonsa, Tinubu:
: Ya godewa ‘yan Najeriya bisa haƙuri da fahimtar da suka nuna, inda ya bayyana cewa ya kamata a sake fasalin kasar nan.
Ya yi nuni da cewa tun da ya Hau mulkin ƙasar nan ya ke futo da tsare-tsaren bunqasa tattalin arziki, da suka haɗa da :
Rage hauhawar farashin kayayyaki: An fara samun saukin hauhawar farashin kayayyaki, inda farashin shinkafa da sauran kayan masarufi ke raguwa.
Bangaren Mai da Gas:shugaba Tinubu ya ce Sashin yana murmurewa inda aka samu ƙarin kashi 400% cikin ɗari na zuba hannun jari.
– *Inganta Tsaro , Shugaba Tinubu ya bayyana nasarorin da aka samu wajen dawo da zaman lafiya a wasu yankunan Arewa maso Yamma, da rage barazanar rayuwa da da kuma ceto ‘yan kasar da aka sace.
*Gyaran Haraji*: Ya bayyana sabon tsarin haraji da nufin rage yawan haraji, tallafawa kananan ‘yan kasuwa, da inganta tattalin arziki.
Shugaba Tinubu ya kuma tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa, Nan gaba kaɗan za a kara fahimtar irin Tsare-tsaren gwamnati da kuma cigaba da walwala wanda ke tafe kuma ‘yan Najeriya za su ji daɗinsa .