Hausa News

‘Yansanda a Kano sun kama wanda ake zargi da Kashe matar aure.

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wanda ake zargi da laifin kisan wata mata ‘yar shekara 22 da haihuwa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da samun gagarumar nasara a wani lamari na kisan gilla da ya faru a ranar 6 ga Afrilu, 2025, a Tsamiyar Duhuwa, da ke Kano. Bayan gudanar da bincike mai zurfi da amfani da fasarhar zanani  ‘yan sanda sun kama babban wanda ake zargi,  Mai suna Shu’aibu Abdulkadir, mai shekaru 35, a ranar 23 ga Mayu, 2025.

A cewar rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ya amince da kutsawa cikin gidan auren wanda aka kashen, inda ya shake ta, tare da daba mata wuka a wuya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarta. Matar mai suna Rumaisa Haruna mai shekaru 22, mijinta, Ibrahim Mohammed ne ya gano ta da mugun rauni a wuyansa, kuma an tabbatar da mutuwarsa a asibiti.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yabawa jami’an bincikenta  bisa namijin ƙoƙarin da suka yi da sanin makamar aiki da ya kai ga cafke wanda ake zargin. Wanda ake zargin a halin yanzu yana tsare kuma yana taimakawa wajen gudanar da bincike don tabbatar da an yi cikakken adalci.

 

  1.  Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya buƙaci jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suka shafi ‘yan sanda. Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa al’umma ƙudurin ta na ganin ta kare dukkan mazauna jihar da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top